IQNA

Majalisar Dinkin Duniya Ta Sanar Da Amincewarta Da Majalisar Libya

15:41 - September 18, 2011
Lambar Labari: 2189378
Bangaren kasa da kasa, majalisar dinkimn duniya ta amince da majalisar rikon kwaryar kasar Libya a matsayin bangaren da ke wakiltar al'ummar kasar a hukumance, kamar kwamitin tsaro ya bukaci a janye takunkumin da aka dora ma kasar.


Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto wani rahoto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar Aljazeera cewa, majalisar dinkimn duniya ta amince da majalisar rikon kwaryar kasar Libya a matsayin bangaren da ke wakiltar al'ummar kasar a hukumance, kamar kwamitin tsaro ya bukaci a janye takunkumin da aka dora ma kasar a lokacin da Gaddafi yak ekan karagar mulki.

Wani labarin kuma yana yin ishara da cewa Kakakin hambararriyar gwamnatin Gaddafi ta Libiya ya sanar da cewar mutane 354 ne suka rasa rayukansu sakamakon hare haren jiragen saman yakin kungiyar NATO kan garin Sirt.
Kakakin hambararriyar gwamnatin kasar Libiya ta Mu'ammar Gaddafi Musa Ibrahim ya bayyana cewar a cikin dare guda hare hare wuce gona da iri da jiragen saman yakin kungiyar tsaro ta NATO suka kai kan garin Sirt sun yi sanadiyyar mutuwan mutane 354 tare da jikkata kimanin 700 na daban saboda sun kai hare haren ne kan gidajen fararen hula da otel a cikin garin na Sirt.
Musa Ibrahim ya kuma kara da cewar a cikin kwanaki 17 da suka gabata jiragen saman yakin na kungiyar tsaro ta NATO sun kashe mutane fiye da 2000 a cikin garin na Sirt har ila yau Musa Ibrahim ya yi da'awar cewa Mu'ammar Gaddafi da kansa n eke jagorantar yaki da masu bore a garin na Sirt karshen tungarsa da magoya bayansa a kasar Libiya.
862049


captcha