Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadrawa na yanar gizo cewa, shafin sadarwa na danger room ya tona a sirin 'yan sandan kasar Amurka wato FBI dangane da irin rawar da suke takawa wajen kara tunzura mutane su kyamaci musulunci a cikin kasar ta Amurka.
Wani rahoton kuma ya yi ishara da cewa Matsalar basussukan da kasashe masu amfani da takardar kudi ta Yuro suke fama da ita tana fallasa alakar da ke akwai tsakanin gwamnatocin kasashen da kasuwannin da suka shiga rudani, kamar yanda wasu masana tattalin arziki suka bayyana.
Rahotanni daga birnin Paris sun habarta cewa yan siyasa suna dora laifi a kan kasuwar kudade da masu hada-hadarta, suna cewa wasu masu harakar kudade suna aiki ne wa wata makarkashiya mai kokarin karya takarkudin ta uro.
Amma Marc Touti mai aiki da kamfanin Assya Compagnie na hada-hadar kudade ya ce a banza gwamnatoci suke sukar kasuwanni domin kuwa rikicin basussukan da ake fama da shi a nahiyar Turai sakamako ne na kurakurai da yan siyasa suka tafta na tsawon shekaru goma.
Touti ya ce gwamnatocin kasashen sun kasa daukar kwararan matakai kamar rage karbar basussuka da rage gibin kasasfin kudi, da kuma daidaita haraji don ya dace da yanayin maaikata.
862149