Bangaren kas ada kasa, an kafa wani kwamiti da zai kula da shirya taruka na kasa da kasa kan fadakar musulmi da zai rika gudanar da zama domin tattaunaw akn ci gaban da al’ummomin musulmi suke samu ta wannan fuska.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talajin din Al-alam an bayyan acewar an kafa wani kwamiti da zai kula da shirya taruka na kasa da kasa kan fadakar musulmi da zai rika gudanar da zama domin tattaunawa kan ci gaban da al’ummomin musulmi suke samu ta wannan fuska musamman ma ganin yadda al’ummomin kasashen larabawa suka mike domin neman sauyi a cikin harkokin siyasa da mulki a kasashensu.
Rahoton ya ci gaba da cewa babban aikin wannan kwamiti shi ne sa ido kan yadda al’ummomin musulmi suke mikewa domin neman ‘yancinsu, tare da ba su shawarwari kan yadda za su kaucewa fadawa cikin tarkon makiya masu kokarin ganin sun karkatar da yunkurin al’ummomin larabawa zuwa ga maslaharsu da kuma ta haramtacciyar kasar Isra’ila.
Ko shakka babu kafa wani kwamiti da zai kula da shirya taruka na kasa da kasa kan fadakar musulmi da zai rika gudanar da zama domin tattaunaw akn ci gaban da al’ummomin musulmi suke samu ta wannan fuska, hakan na da matuka muhimmanci ta kowace fuska ga masu yunkurin.
863102