IQNA

Masu Bore A Libya Sun Jaddada Rashin Amincewa Da Shiga Cikin Harkokinsu

20:42 - September 19, 2011
Lambar Labari: 2190184
Bangaren kasa da kasa, masu bore a kasar Libya sun jaddada cewa ba su amince da duk wani yunkuri na shiga cikin harkokinsu na cikin gida ba daga bangarorin ketare domin kuwa juyinsu na mutanen Libya ne baki daya.
Kamfanin diallncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga tashar talabijin ta Allam dake watsa shirinta kan tauraron dan adam daga Tehran cewa, daya daga cikin jagororin juyin juya hali a Libya ya bayyana cewa masu bore a kasar Libya sun jaddada cewa ba su amince da duk wani yunkuri na shiga cikin harkokinsu na cikin gida ba daga bangarorin ketare domin kuwa juyinsu na mutanen Libya ne baki daya kuma ba su da niyyar barin kasashen waje su yi musu shigar shugula.
Ya Bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da jawabinsa agaban taron fadakar musulmi na duniya da aka gudanar a birnin Tehran fadar mulkin jamhuriyar muslunci ta Iran, wanda ya samu halartar masana akalla dubu daya daga kasashen duniya tamanin, inda aka gabatar da wabai da bayar da shawarwari masu bore a kasashen musulmi da na larabawa.
Tun wanna lokacin dai masu bore a kasar Libya sun jaddada cewa ba su amince da duk wani yunkuri na shiga cikin harkokinsu na cikin gida ba, bisa la’akari da yadda wasu kasashen yammacin turai har da na larabawa suka nuna kadayinsu a cikin arzikin da Allah ya huwace musu.
862982

captcha