Bangaren kasa da kasa, a jiya masallatai a fadin kasar Faransa sun karbi bakuncin dubban mutane da ba musulmi ba, domin nuna musu al’adu irin na musulmi da musulunci ya koyar da su.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na mosquee-lyon cewa a jiya masallatai a fadin kasar Faransa sun karbi bakuncin dubban mutane da ba musulmi ba, domin nuna musu al’adu irin na musulmi da musulunci ya koyar da su bisa akidarsa da kuma abin da ya ginu kansa.
Bayanin ya ci gaba da cewa an saba gudanar da irin wannan a cikin kowace shekara akasar ta Faransa, wadda iat ce kasar turai da ta fi kowace kasa yawan musulmi, kuma babbar cibiyar bunkasa harkokin musulunci a yankin nahiyar turai ce ta dauki nauyin shirya wannan taro a masallatan.
A jiya da kuma safiyar yau masallatai a fadin kasar Faransa sun karbi bakuncin dubban mutane da ba musulmi ba, domin nuna musu al’adu irin na musulmi, wanda kuma hakan na da gagarumin tasiri a cikin irin wannan lamari kamar dai yadda wasu da suka halraci wasu masallatan suka bayyana.
862987