Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: jami'an tsaron gwamnatin Ali Abdallah Salih a wani hari da bude wuta da suka yi kan masu zanga'zangar neman kwo sauyi a birnin San'aa fadar mulkin kasar Yaman mutane ashirin ne suka rasa rayukansu day a hada da wasu kananan yara biyu.A ranar ashirin da takwas ga watan Shahrivar shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in ne shekara ta hijira shamsiya jami'an tsaron gwamnatin Ali Abdallah Salih suka budewa masu zanga-zangar wuta da hakan yayi sanadiyar rasuwar mutane ashiri day a hada da kananan yara biyu lamarin da ya jawo suka daga kasashen da kungiyoyi na duniya.
864696