Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: a jiya ne ashirin da tara ga watan Shahrivar na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya a garin Marsail da ke kudu maso gabacin Faransa aka yi wa karamin ofishin jakadancin Haramtacciyar kasar Isra'ila barazana kai masa harin Bam.Jim kadan da jin wannan labari sai jami'an tsaro nay an sanda suka kai wa ginin dauki da yi masa binciken ganin kokob da binciken motocin da ke ciki da wajan ginin. A ranar sha takwas ga watan shahrivar da muke ciki ma a birnin Alkahira fadar mulkin kasar Masar an kaiwa ofishin jakadancin Haramtacciyar kasar Isra'ila a Masar hari.
864690