Bangaren kasa dakasa; a birnin Liyon na kasar faransa a ranar talatin da daya ga watan Shahrivar shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya za a fara gudanar da wani mihimmin taron na tattaunawa da fahimtar juna tsakanin addinai inda malaman addinan dam asana za su kasance a cikin zauren taron domin fahimta da tattaunawa.
Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: a birnin Liyon na kasar faransa a ranar talatin da daya ga watan Shahrivar shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya za a fara gudanar da wani mihimmin taron na tattaunawa da fahimtar juna tsakanin addinai inda malaman addinan dam asana za su kasance a cikin zauren taron domin fahimta da tattaunawa.Gudanar da irin wannan taro nada matukar muhimmancin gaskiya musamman a daidai wannan lokaci da zamani da duniya da al'ummomi ke fuskantar tashe-tashen hankula da zubar da jinni da kuma makiyan addinan ke amfani da tada fitina a tsakanin mabiya addinan a kasashe daban daban naduniya.
864549