Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: jaridar Sandi Telegram da ake bugawa a kasar Britaniya ta kawo labarin ganawa ta sirri da aka yi tsakanin Toni Bleya tsohon firaministan kasar da kuma shugaban kasar Libiya da aka hambare . Har ila yau an kawo labarin wasu ganawa har sau biyu a boye da Bleyan ya yi da shugaban na kasar Libiya Mu'ammar Kaddafi a shekara ta dubu biyu da takwas miladiya da kuma shekara ta dubu biyu da tara miladiya.
864191