Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na ayanr gizo na jaridar yaum Sabi cewa babban malamin jami’ar Azhar ta kasar Masar Ahmad Tayyib ya bukaci mahukuntan kasar da su amince da kasar palastinu a hukumance a zaman babban zauren majalisar dinkin duniya da yake gudana ahalin yanzu tare da halartar wakilai na dukkanin kasashen duniya.
A cikin shirye-shiryen da suka gabata, ayoyi da dama sun yi mana ishara da cewa sharadin samun kyakyawan sakamako daga Allah shi ne imani da aiki na gari, wadannan ayoyi suna bayyana abin da ke cikin zuciyar mumini salihi na daga imani da mika wuya ga Allah, domin shi imani yana cikin zuciya ba abin da mutum ke fada da bakinsa ba kawai, domin kwa sau da yawa mutum zai iya bayyana imani a cikin ayyukansa amma cikin zuciyarsa ba mumini ba.
A lokacin da aikin mutum ya yi daidai da abin da ke cikin zuciyarsa na imani, a lokacin ne ya cika mumini, domin kuwa Allah madaukakin sarki yana kallon abin da ke cikin zukatan talikai ne.
866232