IQNA

Palastinawa Sun Mika Takardar Neman Amincewa Da Kafa Kasarsu

15:48 - September 24, 2011
Lambar Labari: 2192367
Bangaren kasa da kasa, palastinawa sun mika takardar neman amincewa da kafa kasarsu mai cin gishin kanta ga babban sakataren majalisar dinkin duniya domin ya mika wannan takarda ga kwamitin tsaron majalisar domin kada kuri’a kan hakan.
Kamfanin diallncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin din Almanar dake watsa shirye-shiryenta kan tauraron dan adam daga birnin Beirut na kasar Lebanon cewa, shugaban palastinawa Mahmud Abbas tare da tawagarsa, sun mika takardar neman amincewa da kafa kasarsu mai cin gishin kanta ga babban sakataren majalisar dinkin duniya domin ya mika wannan takarda ga kwamitin tsaron majalisar domin kada kuri’a kan hakan domin amincewa ko rashin amincewa.
An mika wannan takarda kafin gabatar da jawabin shugaban palastinawa Mahmud Abbas a gaban wannan taro, wanda ga dukaknin alamu kasashen duniya sun nuna matukar gamsuwarsu da wannan mataki, inda suka yi rafsa masa tabi a lokacin da yake gabatar da jawabin nasa.
Tun kafin lokacin dai gwamnatin Amurka ta fito karara ta nuna rashin amincewarta da duk wani mataki da zai bayar da damar kafa kasar palastinu mai cin gishin kanta, kuma ta sha alwashin yin fatali da wannan magana matukar dai aka gabatar da ita a gaban kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya.
866242

captcha