IQNA

Dan Majalisar Holand Mai gaba Da Addini Ya Yi Kira Da Hana Gina Masallatai

15:46 - September 24, 2011
Lambar Labari: 2192368
Bangaren kasa da kasa, dan majalisar dokokin kasar Holland di nan mai tsananin gab ada addinin muslunci ya yi ga gwamnatin kasar da ta dauki matakan hana gida masallatai a kasar.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Iresh Times cewa, Wilders Geertz dan majalisar dokokin kasar Holland di nan mai tsananin gab ada addinin muslunci ya yi ga gwamnatin kasar da ta dauki matakan hana gida masallatai a kasar baki daya, domin hana ma musulmi gudanar da harkokinsu yadda suke so.
Ya furta hakan ne a ranar alhamis din da ta gabata a lokacin da majalisar dokokin kasar ta Holland take gabatar da zamanta, inda ya ce wajibi ne kasar ta dauki matakn yin koyi da gwamnatin Switzerland wajen hana gina masallatai a kasar, domin hana musulmi walwala wajen gudanar da addininsu.
Wannan mutumin dai kowa ya sn shi da tsananin gaba da addini muslunci, kamar yadda ya yi abubuwa da dama na nuna kyama ga musulmi hakan ba abin mamaki ba ne ga dukaknin musulmin kasar Holland da ma na kasashen yammacin turai,kuma ana tsammanin da dama daga cikin ‘yan majalisar ba za su amince da maganarsa ba domin sun san matsayinsa dangane da musulunci.
A cikin shekara ta 2008 ya rubuta wani littafi mai suna fitina, inda ya ci mutuncin kur’ani mai tsarki a cikinsa, wanda hakan ya harzuka dukkanin musulim a fadin dunya baki daya, inda aka yi ta gudanar da zanga-zangar la’antarsa. 866251
captcha