IQNA

An Gudanar Da Janazar Tsohon Shugaban Kasar Afghanistan Burhanuddin Rabbani

15:44 - September 24, 2011
Lambar Labari: 2192372
Bangaren kasa da kasa, an gudanar da janazar tsohon shugaban kasar Afghanistan Burhanuddini Rabbani kuma shugaban majalisar koli ta sulhu da fahimtar juna a kasar bayan kai harin ta’addanci a kansa a gidansa da ke birnin Kabul fadar mulkin kasar.
Kamfanin diallncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na alwafd cewa, an gudanar da janazar tsohon shugaban kasar Afghanistan Burhanuddini Rabbani kuma shugaban majalisar koli ta sulhu da fahimtar juna a kasar bayan kai harin ta’addanci a kansa a gidansa da ke birnin Kabul bayan da wani mutum ya bukaci ganinsa a matsayi wakilin Taliban, wanda ya tarwatsa kansa a wurin.
Taron janazar ya samu halartar dubban mutane da suka hada da manyan jami’an gwamnatin afghanistan da suka hada da shugaban kasar Hamid karazai, da kuma wasu manyan baki daga kasashen ketare a cikin tsauraran matakai, an gudanar da janazar a masallaci Ark dake birnin kabul.
A lokacin da yake gabatar da jawabi a wajen taron janazar shugaban kasar Afghanistan Hamid Karazai ya bayyana burhanuddini Rabbani a matsayin wani gwarzo wanda ya yi shada a tafarkin gaskiya da neman sulhu da zaman lafiya atsakanin dukkanin al’ummar musulmi ta kasar Afghanistan.
Ya jaddada cewa zai ci gaba da gudanar ada abin da yake yi na neman sulhu da kungiyar taliban domin kawo karshen zaman zullumi da rashin tabbas a kasar baki daya, wanda hakan ba zai yiwu matukar dai ba a yi sulhu da Taliban ba.
866195

captcha