IQNA

An Damke Tsohon Pira Ministan Kasar Libya A kasar Tunisia

15:45 - September 24, 2011
Lambar Labari: 2192373
Bangaren kasa da kasa, rahotanni daga kasar Tunisia sun habarta cewa mahukuntar kasar sun bayar da tabbacin cewa an damke tsohon pira ministan kasar Libya a ranar laraba da ta gabata a kasar.
Kmfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakaltoo daga shafin sadarwa na yanar gizo na acturank cewa rahotanni daga kasar Tunisia sun habarta cewa mahukuntar kasar sun bayar da tabbacin cewa an damke tsohon pira ministan kasar Libya a ranar laraba da ta gabata a kasar bayan da ya sulale daga kasar Libya.
A bangare guda kuma shugaban kasar Lebanon Micheil Sulaiman ya jadda batun makomar Imam Musa a lokacin da yake gabatar da jawabinsa a gaban baban taron majalisar dinkin duniya wanda ke samun halartar shugabannin da wakilan kasashen duniya baki daya.
Ya ci gaba da cewa kasar Lebanon tana jiran gwamnatin ‘yan tawayen kasar Libya ta yi bayani dangae da makomar Imam Musa Sadr, wanda tsohon shugaban mulkin kama karya na kasar Libya Mu’ammar Gaddafi ya kame shi tun kimanin shekaru sama da talatin da suk agabata, kuma har yanzu ba a san makomarsa ba da mutanen da yake tare su.
Gaddafi dai yaki yin bayani dangane da Imam Musa Sadr tun bayan da ya kame shi a lokacin da ya aike masa da goron gayyata a cikin a shekara ta 1978, inda dag abisani bayan da ya fuskanci matsin lamba ya bayyana cewa ya bar kasar ya nufi kasar Italia, lamarin kasar Italia ta karyata.
866180

captcha