Bangaren kasa da kasa: a karo na biyar za a fara taron kungiyar hadin kan gidajen radiyoyi da talbijin na kasashen musulmi da aka bude a jiya talata hudu ga watan Mihir na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya a dakin taro na kasa da kasa da gidan radiyo da talbijin na jamhuriyar musulunci a birnin Tehran fadar mulkin kasar .
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; a karo na biyar za a fara taron kungiyar hadin kan gidajen radiyoyi da talbijin na kasashen musulmi da aka bude a jiya talata hudu ga watan Mihir na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya a dakin taro na kasa da kasa da gidan radiyo da talbijin na jamhuriyar musulunci a birnin Tehran fadar mulkin kasar . a kowa ce shekara ana gudanar da irin wannan taro ne a nan birnin Tehran na jamhuriyar musulunci ta Iran a kowa ce shekara inda shugabanni da wakilan gidajen radiyoyi daga kasashen musulmi da na nan cikin gidan ke haduwa domin tattauna yadda za su inganta ayyukansu da kuma yadda za su tunkari kalubale da barazana daga ketare.
867400