Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin Al-manar cewa, kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah a kasar Lebanon ta fitar ta yi kakakusar suka tare da yin Allawadai da harin bam din da aka kai birnin karbala mai albarma wanda ya ya yi sanadiyar shahadar mutane da dama da kuma jikkatar wasu.
Boma bomai guda biyu sun tarwatse a birnin Karbala mai tsarki na kasar Iraqi a yau lahadi, inda suka kai mutane akalla 25 ga shahada.Dan rahoton gidan television na Presstv ya bayyana cewa bom na farko ya tashi ne a cikin wata mota wacce aka tsaida kusa da ofishin bada katin shaidar zama dan kasa, a yayinda mutanen sukayi cinkoso suna karban katin a safiyar yau lahadi.
Bom na biyu kuma ya tashi ne a lokacinda wani dan kunan bakin wake ya tarwatsa kansa a cikin wadanda suka zo don taimakawa wadanda bom na farko ya rutsa da su.
Birnin Karbala mai tsarki dai baya rabuwa da masu ziyarar hubbaren Imam Husain (a) jikan manzon Allah (s) daga ciki da kuma wajen kasar ta Iraqi a duk tsawon shekara.
Babu wanda ya dauki nauyin hare haren na yau, kuma akwai yi yuwar adadin wadanda zasu mutu ya karu.
Tun lokacinda kasar Amurka ta mamaye kasar Iraqi a shekara ta 2003 ne dai irin wadannan hare hare suka kunno kai.
867572