Bangaren kasa da kasa, an fara gudanar da gasar karatun kur'ani ta daliban makarantun sakandare a bangarori daban–daban na kasar Iraki daga jiya, kuma gasar za ta ci gaba har tsawon kwanaki hudu a nan gaba.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Zi Qar da ake bugawa a kasar Iraki cewa an fara gudanar da gasar karatun kur'ani ta daliban makarantun sakandare a bangarori na kasar Iraki daga jiya, kuma gasar za ta ci gaba har tsawon kwanaki hudu a nan gaba, duk kuwa da cewa ya zuwa yanzu an bude gasar ne yankin Kazimain.
Shakka babu aikin da ya ke zama karbabbe shi ne wanda aka yi da tsarkin niyya saboda Allah, domin kuwa wannan irin aikin yana nuni ne da imani na hakika da kuma nesantar duk wani nau'i na shirka wannan ayar tana yin nuni ne da cewa halin mutum na son ya mallaki kowai ya kai shi ga nuna cewa Ubangiji ma yana tare da shi ne shi kadai, ba waninsa ba.
Yana daukar cewa Ubangiji nashi ne shi kadai ba na waninsa ba, alhali kuwa shi Ubangiji bai kebanta mabiyan wani addini ne ko wata zuriya ko wata kabila ba, Ubangiji na dukkanin talikai ne.
867697