IQNA

Musulmin Birtaniya Sun Bayar Da Gudunmuwar Kudi Ga Asibitocin Kasar

19:01 - September 27, 2011
Lambar Labari: 2194557
Bangaren kasa da kasa, musulmin kasar Birtaniya sun bayar da gudunmawar kudade ga asibitoci biyu na garin Lanshair da suka kai yuro dubu hamsin da bakwai 57000 da nufin bunkasa ayyukan jin kai da suke gudanarwa a kasar.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na trouvetammosquee cewa musulmin kasar Birtaniya sun bayar da gudunmawar kudade ga asibitoci biyu na garin Lanshair da suka kai yuro dubu hamsin da bakwai da nufin bunkasa ayyukan jin kai da suke gudanarwa a kasar wadanda dama sun saba gudanar da su tsawon shekaru.
A bangare guda kuma Wata majiyar tsaron kasar Masar ta bayyana cewar wasu mutanen da ba a san ko su wane ne ba sun tarwatsa daya daga cikin bututun da ke daukan iskar gas daga kasar zuwa HKI da sanyin safiyar nan.

Kamfanin dillancin labaran AFP ya nakalto wata majiyar tsaron kasar Masar din tana cewa fashewar ta faru ne a safiyar yau din nan talata a wani waje kusa da garin Al-Arish da ke arewa da yankin Sinai. Wata majiyar ta ce wasu mutane ne dauke da makamai suka bude wuta kan bututun lamarin da ya sanya shi fashewa.

Wannan dai shi ne irin wannan hari na shida da aka kai wa irin wadannan bututu da ke daukar iskar gas din zuwa HKI tun bayan kifar da gwamnatin tsohon dan mulkin kama-karya na kasar Hosni Mubarak a watan Fabrairun da ya wuce.

Mafi yawa daga cikin al'ummar kasar Masar suna adawa da sayar da iskar gas din kasar ga HKI da gwamnatin Mubarak din take yi.
867551
captcha