Bangaren kasa da kasa: Jagororin musulmi a kasar Indonosiya a ranar hudu ga watan Mehr shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shasiya sun fitar da wani bayani da a cikinsa suke yin Allah wadai da harin ta'addancin da aka kai wa cocin kiristocin tarikar Protastan a garin Sulu .
Kamfanin dillancin labaran Ikna da ke kula da watsa labaran harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musuluncin ta Iran ne ya watsa labarin cewa; Jagororin musulmi a kasar Indonosiya a ranar hudu ga watan Mehr shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shasiya sun fitar da wani bayani da a cikinsa suke yin Allah wadai da harin ta'addancin da aka kai wa cocin kiristocin tarikar Protastan a garin Sulu . wannan harin ta'addanci ya jawo jikkatar kirsitci ashirin da bakwai da kuma ake ganin wani makirci ne na haddasa rikicin kabilanci da na addini a wannan kasa.
868379