Bangaren kasa da kasa; musulmin Cana duk da cewa suna rayuwa ne a wani yanki mai kwarkware yanci a kasar amma tsarin koyarwa na gwamnatin Kominisanci a Cana na tashi fadin ganin ya soke tsarin koyar da Kur'ani da karatun addini a makrantu da jami'o'I lamarin da musulmin Cana suka ce sam ba za ta sabu ba.
Kamfanin dillancin labaran Ikna da ke kula da watsa labaran harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musuluncin ta Iran ne ya watsa labarin cewa; musulmin Cana duk da cewa suna rayuwa ne a wani yanki mai kwarkware yanci a kasar amma tsarin koyarwa na gwamnatin Kominisanci a Cana na tashi fadin ganin ya soke tsarin koyar da Kur'ani da karatun addini a makrantu da jami'o'I lamarin da musulmin Cana suka ce sam ba za ta sabu ba.Yankuna biyar da aka bawa yancin rayuwa da tsari mai kwarya-kwaryar yanci a kasar Cana da suke da tsarin koyar da kur'ani ga yara a kananan makarantu na firamirai da na sakandari amma sai gashi tana kasa tana dabo domin kuwa a halin da ake ciki gwamnatin kominisanci a Cana na raya cewa wadannan yanki biyar komar sauran yankuna hamsin da biyar na kasar dole su tafi karkashin tsarin koyarwa na bai daya ba tare da nuna bambanci da wariya ba lamarin da masu bin diddigin lamarin ke kollonsa a matsayin zagon kasa .
868340