IQNA

Ministan Tsaro Na Kasar Yamen Ya Tsallaka Rijiya Ta Baya

12:06 - September 28, 2011
Lambar Labari: 2194900
Bangaren kasa da kasa: Muhammad Nasir Ahmaed Ali ministan tsaro na kasar Yamen a jiya ne biyar ga watan Mehr na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya ya tsallaka rijiya ta baya a wani yunkurin kasha shi a garin Adan da ke kuduncin kasar ta Yamen.




Kamfanin dillancin labaran Ikna da ke kula da watsa labaran harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musuluncin ta Iran ne ya watsa labarin cewa; Muhammad Nasir Ahmaed Ali ministan tsaro na kasar Yamen a jiya ne biyar ga watan Mehr na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya ya tsallaka rijiya ta baya a wani yunkurin kasha shi a garin Adan da ke kuduncin kasar ta Yamen.An kai masa hari ne da wata mota da aka makure da bama-bamai a kan hanyar da tawagarsa ke wucewa a Garin Adan inda mutane goma daga cikin wadanda ke tare da tawagar ta ministan tsaro suka jikkata amma Mohammed Nasir Ahmed Ali ba tare day a samu kwarsane ba.

868555

captcha