Bangaren kasa da kasa, tsohon shugaban mulkin kama karya na kasar Masar Husni Mubarak ya nuna matukar tsoronsa dangane da kafofin yada labarai na musulunci wadanda suke bayyana hakikanin gaskiya dangane da ta’addancin haramtacciyar kasar Isra’ila.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakaltoo daga shafin sadrawa na yanar gizo na na jaridar Ahram da ak e buugawa akasar Masar cewa, daya daga cikin fitattun marubutan jaridar Ahmad Al-suyufi ya bayyana cewa, a lokacin mulkinsa tsohon shugaban mulkin kama karya na kasar Masar Husni Mubarak ya nuna matukar tsoronsa dangane da kafofin yada labarai na musulunci wadanda suke bayyana hakikanin gaskiya dangane da ta’addancin haramtacciyar kasar Isra’ila da kuma abin da yake aikatawa kan musulmi masu kalubalantar Amurka a kasarsa da yankin baki daya.
Ya ci gaba da cewa irin rawar da Mubarak ya taka lokacin mulkinsa ta yi muni matuuka da nufin murkushe duk wani yunkurin jama’a da ya shafi neman ‘yancinsu daga mulkin zalunci da fir’anancin, wanda kasashenyammacin turai gami da munafukan larabawa suke bashi cikakken goyon baya kan hakan.
Ko shakka babu tsohon shugaban mulkin kama karya na kasar Masar Husni Mubarak ya nuna matukar tsoronsa dangane da kafofin yada labarai na musulunci wadanda suke bayyana hakikanin gaskiya dangane da ta’addancin yake aikatawa alokacin mulkin nasa.
868709