IQNA

Za A Yi Wani Fim Mai Suna Al-Hussain A Birnin Karbala Mai Alfarma

21:09 - September 29, 2011
Lambar Labari: 2195582
Bangaren kasa da kasa, daya daga cikin masu shiya fim a kasar Iraki ya sheda cewa yanzu haka suna shirin fitar da wani fim kan Imam Hussain (AS) jikan manzon Allah dauke da sahihin tarihinsa da kuma ahlul bait.


Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, Sahib Al-hasnawi daya daga cikin masu shiya fim a kasar Iraki ya sheda cewa yanzu haka suna shirin fitar da wani fim kan Imam Hussain (AS) jikan manzon Allah dauke da sahihin tarihinsa da kuma ahlul bait (AS) da bayyana hakikanin abin da ya faru a kansu an zalunci a tsawon tarihi.

Ya ci gaba da cewa bisa la'akari da yadda wasu suke ta hankoron ganin cewa sun boye hakika dangane da abin da ya faru a cikin tarihi, ya zama wajibi kan masu sauran lamiri daga cikin musulmi, musamman ma mabiya ahlul bait, su fito da hakikanin abin da ya faru ta dukaknin hanyoyi.

Sahib Al-hasnawi daya daga cikin masu shiya fim a kasar Iraki ya sheda cewa yanzu haka suna shirin fitar da wani fim kan Imam Hussain (AS) jikan manzon Allah dauke da sahihin tarihinsa da kuma ahlul bait da kuma bayyana matsayinsu a cikin addini.

869004





captcha