Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na kamfanin dilalncin labaran SABA na kasar Yemen cewa, a cikin gaba da mayar da martanin kasashen duniya kungiyar tarayyar turai ta bukaci haramtacciyar kasar Isra'ila da dakatar da shirin da take da shi na gina wasu sabbin matsugunnai a cikin yankunan palastinawa.
A Bangare guda kuma yan sandan gwamnatin Yahudawan Sahyoniya sun kame dan majalisa dan kungiyar Hamas Ahmad Attoun wanda ya shafe sama da shekara guda yana fakewa a ofishin kungiyar Red Cross a gabashin birnin Kudus.
Attoun ya fake ne a ofishin na kungiyar Red Cross tare da wasu 'ya'yan kungiyar biyu mazauna birnin Kudus, daya dan majalisa daya kuma jamiin gwamnatin Hamas, bayan da hukumomin Haramtacciyar Kasar Israila suka soke izinin zamansu a wannan birni.
A wata sanarwa da suka fitar bayan da yan Sahyoniyan suka soke izinin zamansu a birnin a watan Yunin bara, mutanen ukun sun bayyana cewa su 'ya'yan birnin Kudus ne kuma zasu ci gaba da zama a cininsa ba inda za su.
Kungiyar Red Cross dai ta jaddada wa gwamnatin Israila cewa korar Palasdinawa daga gidajensu ya saba wa dokokin kasa da kasa.
869125