IQNA

Haramtacciyar Kasar Isra'ila Ta Killace Gabar Yamma da Kogin Jordan

21:11 - September 29, 2011
Lambar Labari: 2195588
Bangaren kasa da kasa, haramtacciyar kasar Isra'ila ta dauki matakan killace dukaknin yankunan palastinawa da suke gabar yamma da kogin Jordan a lokacin da take shirin gudanar da bukukuwan idin yahudawa.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na radiosawa cewa haramtacciyar kasar Isra'ila ta dauki matakan killace dukaknin yankunan palastinawa da suke gabar yamma da kogin Jordan a lokacin da take shirin gudanar da bukukuwan idin yahudawa a cin 'yan kwanakin nan.

Bayanin ya ci gaba da cewa kungiyoyin palastinawa yan gwagwarmaya da suke yankin zirin Gaz ad ama yankunan gabar yamma da kogin Jordan sun ja kunnen haramtacciyar kasar Isar'ila kan ta shiga taitayinta, dangane da shishigin da take son yi kan al'ummar palastinu a wannan lokaci.

Haramtacciyar kasar Isra'ila ta dauki matakan killace dukaknin yankunan palastinawa da suke gabar yamma da kogin Jordan a lokacin da take shirin gudanar da bukukuwan idin yahudawa kamar yadda ta saba gudanarwa a kowace shekara.

869063


captcha