IQNA

Jiragen Isra’ila Sun Yi Ruwan bamabamai Kan yankin Zirin Gaza

14:41 - October 01, 2011
Lambar Labari: 2196579
Bangaren kasa da kasa, jiragen yaki na haramtacciyar kasar Isra’ila sun yi ruwan bama-bamai a kan yankunan zirin Gaza a cikin daren jiya da nufin firgita falastinawa da suke fatan ganin sun kafa kasar palastinu mai cin gishin kanta.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani rahoto da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin din Al-alam a ci gaba da aikata ayyukan ta’addancin yahudawan sahyuniya jiragen yaki na haramtacciyar kasar Isra’ila sun yi ruwan wuta a kan yankunan zirin Gaza a cikin daren jiya da nufin firgita falastinawa da suke fatan ganin sun kafa kasar palastinu mai cin gishin kanta kamar yadda shugaban palastinawa ya gabatar wa majalisar dinkin duniya.
Bayanin ya ci gaba da cewa wannan matakin da yahudawan sahyuniya suka dauka yan atattare da sakonni ga shugabannin palastinawa da suke ta fadi tahin ganin kasashen duniya sun amince da kafa kasar palastinu guda daya mai cin gishin kanta.
A tsakar daren jiya har zuwa asubashin yau jiragen yaki na haramtacciyar kasar Isra’ila sun yi ruwan bama-bamai a kan yankunan zirin Gaza a cikin daren jiya da nufin firgita falastinawa da suke fatan ganin sun kafa kasar palastinu mai cin gishin kanta a cikin lokutan nan, duk kuwa da rashin amincewar Amurka da wasu munafukan kasashen turai.
870131

captcha