Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na tashar talabijin ta Aljazeera cewa, babban sakataren kwamitin bayar da kyutykan sulhu na kasa da kasa ya sheda cewa za a bayar da kyautuka na musamman da suka hada da kyautar sulhu ta nobel ga masu fafutukar neman 'yanci na demokradiyya a cikin kasashen larabawa da na musulmi.
A wani labarin kuma masu gudanar da ayyukan agaji a kasar Libya sun bayyana cewa sama da mutane 50,000 ne aka tsugunnar a wurare daban-daban bayan da suka gudu suka bar gidajensu a garuruwan Sirt da Bani Walid.
Mai Magana da yawun kungiyar bayar da agaji ta Hilal Ahmar a kasar Libya Abdulhamid Madani, ya sheda cewa sun tsugunnar da dubban mutanen a yankunnan Haisha, da Washka da kuma Wadi Zamzam da ke tsakanin biranan Sirt da kuma Misrata, yayin da wasu daruruwa kuma aka tsugunnar da su a wasu tantuna da aka kafa a garin Bingazi.
Rahotanni daga Libya sun tabbatar da cewa dakarun 'yan tawayen kasar Libya suna fuskantar turjiya mai tsanani daga dakarun da ke biyayya ga kanar Gaddafi a garin Bani Walid, lamarin da ya tilasta mayakan 'yan tawayen ja da baya zuwa wasu yankuna da ke wajen birnin.
870118