IQNA

Wasu Rahotanni Sun Yi Nuni Da Cewa An Damka Kakakin Gaddafi

22:01 - October 01, 2011
Lambar Labari: 2196788
Bangaren kasa da kasa, wasu rahotanni da suke fitowa daga kasar Libya sun ce an damke kakakin hammbararen shugaban mulkin kama karya na kasar Libya Musa Ibrahim a lokacin da yake barin birnin Sirt duk da cewa babu wani tabbaci kan labarin.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar taabijin din Aljazerra cewa, rahotanni da suke fitowa daga kasar Libya sun ce an damke kakakin hammbararen shugaban mulkin kama karya na kasar Libya Musa Ibrahim a lokacin da yake barin birnin Sirt duk da cewa babu wani tabbaci kan labarin domin babu wata kafar yada labari da ta samu tabbaci kan hakan ta hanyar ganinsa ko ganin wanda ya gan shi.

Wani labarin kuma yana cewa Fira ministan kasar Libya Baghadadi Mahamudi ya ce yanzu haka gwamnatin kasar ta soma rubuta wani daftarin doka wanda ya tanadi yi wa illahirin wadanda suke da hannu a rikicin da ake fama da shi a kasar afuwa kamar dai yadda taron shugabannin kabilun kasar da aka gudanar a jiya juma'a a birnin Tripoli ya bukata.

Duk da cewa fira ministan bai bayyana lokacin da gwamnatinsa za ta gabatar wa masu adawa da ita wannan daftari na doka mai yin afuwa ba, to amma ya ce idan har aka tabbatar da ita kamar dai shuwagabannin kabilu da suka halarci wannan taro suka bukata, dokar za ta yi wa bangaren gwamnati da kuma na 'yan adawa afuwa baki daya.

A lokacin da yake yin karin bayani dangane da wannan batu na afuwa, kakakin gwamnatin kasar Libya Moussa Ibrahim ya ce an dora wa shuwagabannin kabilun alhakin yin tattaunawa da 'yan tawaye da kuma kungiyoyin kasa da kasa domin ganin cewa wannan afuwa ta samu karbuwa a cikin gaggawa. To sai dai shuwagabannin kabilun sun bayyana Kaddafi a matsayin karbabben shugaban kasar Libya wanda maciya amanar kasa ke yi wa bore.

870064



captcha