Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a labarin da ya samu daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin dunn al-alam an bayyana cewa, Zaman da komitin tsaro na majalisar dinkin duniya ta gudanar a jiya laraba da nufin kakabawa kasar Syria karin wasu takunkumai ya tashi ba tare da kaiwa ga manufa ba.
Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa AFP ya bayyana cewa, kasashen Britania, Faransa, Jamus da kuma Potigal ne suka gabatar da bukatar kara kakabawa kasar Syria takunkumi. Amma sabawar da kasar Rasha ta yi ga bukatar ya hana ta kai labari.
Jakadan kasar Rasha a majalisar dinkin duniya Vitaly Chukin, ya ce kasar Rasha tana bukatar a warware matsalar kasar Syria ta hanayar tattaunawa ne.
Wasu kasashen yamma karkashin jagorancin Amurka suna taimakawa wasu kungiyoyin yan adawar kasar Syria da makamai, inda suke kashe jami'an tsaron kasar da kuma wani lokacin har da fararen hula.
Har'ila yau wadannan kasashe suna bukatar komitin tsaro na majalisar dinkin duniya ya kara kakabawa gwamnatin Bashar Al-asad takunkumi da nufin kawo karshen shugabancinsa.
Gwamnatin kasar Syria dai, ita ce kadai kasar Larabawa da take tallafawa kungiyoyi masu gwagwarmaya da haramtacciyar kasar Isra'ila a yankin. Wadanda suka hada da kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon da kuma Hamas ta Palasdinawa.
870103