IQNA

Hukumar 'Yan sanda Ta Duniya Ta Bayar Da Sammacin Kame Sa'idi Gaddafi

21:59 - October 01, 2011
Lambar Labari: 2196790
Bangaren kasa da kasa, hukumar 'yan sanda ta kasa da kasa ta fitar da wani sammaci na kame dan shugaban kasar Libya Saidi Gaddafi tare da mika mata shi bisa zargin cewa yan ada hannu a cikin wasu abubuwan barna da aka aikata a kasar Libya.



Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Al-alam cewa hukumar 'yan sanda ta kasa da kasa ta fitar da wani sammaci na kame dan shugaban kasar Libya Saidi Gaddafi tare da mika mata shi bisa zargin cewa yan ada hannu a cikin wasu abubuwan barna da aka aikata a kasar Libya wanda yanzu haka yake boye a wasu yankuna na kasar Niger.

Sa'idi Gaddafi dan shekaru talatin haihuwa ya shiga cikin kasar Niger ne tare da wasu 'yan kabilar abzinawa da suke samun goyon baya da tallafin kudade daga Gaddafi a lokacin da yake kan karagar mulki, inda suka ba shi mafaka acikin yankunansu da suke jahar agadez, amma tuni jami'an gwamnatin jamhuriyar Niger suka sha alwashin cewa ba za su taba mika shi ba.

Hukumar 'yan sanda ta kasa da kasa ta fitar da wannan sammaci ne na kame dan shugaban kasar Libya Saidi Gaddafi tare da mika mata shi bayan da ta ji cewa ya shiga akasar Nigeria, kuma babu wata tuhuma akansa da za ta sanya Niger ta mika shi, amma fitar da wannan samaci ya canja komai.

870107


captcha