Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar al-alam da ke gabatar da shirye-shiryenta a cikin harshen larabci kan tauraron dan adama daga birnin Tehran cewa, mutane ne suka gudanar da wata gagarumar zanga-zangar yin Allawadai da hukuncin da kotun soji ta yanke kan masu zanga-zanga a kasar Bahrain da suka hada da likitoci da jami'an kiwon lafiya, wanda hakan ya yi hannun riga da dokokin kasa da kasa da ma na duniya baki daya.
kotu a kasar Bahrain ta tabbatar da hukunci kan wasu mutane 14 da ake tsare da su saboda dalilai na siyasa, bisa hujjar cewa suna na hankoron kawo karshen mulkin mulukiya a kasar, dukkanin mutanen dai fitattu ne wajen gwagwarmaya ta siyasa a kasar ta Bahrain, da neman ma al'ummar kasar 'yancinsu daga mulkin mulukiya na gidan sarautar Ali-Khalifa.An yanke hukuncin daurin rai da rai a kan wasu daga cikinsu, wasu kuma daurin shekaru 15 a gidan kaso.
Kotun ta ce ta samu mutnanen da laifin tunzura mutane domin su yi zanga-zangar neman sauyi a kasar, da nufin kifar dagidan sarauta da kuma canja kundin tsarin mulki, da kuma hada baki da wasu bangarori na waje.
Wannan mataki da kotun ta dauka ya zo ne a daidai lokacin da mahukuntan kasar ta Bahrain suka kara tsananta matakan murkushe masu zanga-zangar lumana, da suke neman sauyi na demokradiyya a kasar, inda a cikin makon nan jami'an tsaron kasar Bahrain tare da na Saudiyya da suke taimaka musu, suka ci zarafin wasu mata saboda shiga cikin zanga-zangar neman sauyi, lamarin da ya jawo fushin al'ummar kasar da ma sauran musulmi a kasashen duniya daban-daban.
870051