Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cea ya naklato daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Al-dastur cewa, kungiyoyi gami da jam'iyun siyasa akalla talatin ne suka gudanar da wani jerin gwano a cikin birnin Alkahira domin neman sake dawo da matsayin juyin da suka yi wanda ke neman ya zama wani abin wasa a hannun sojoji wadanda suma yara ne ga tsohon shuagaban kasa na kama karya.
A ranar juma'a dubun dubatar mutane ne suka yi cikar kwari a dandalin Tahrir da ke tsakiyar birnin Alkahira na kasar Masar inda suka bayyana bukatarsu na ganin an cire dokar ta baci da aka kafa a kasar sannan kuma da gaggauta shimfida tsarin demokradiyya a kasar.
Duk da cewa tun cikin watan afrilun da ya gabata ne aka kori Husni Mubarak daga kan karagar mulkin kasar, to amma har yanzu dokar ta bacin da shugaban ya kafa fiye da shekaru 30 da suka gabata tana ci gaba da aiki, kuma jami'an tsaron na amfani da ita domin murkushe masu zanga-zanga sannan kuma bangaren shara'a na yanke wa jama'a hukunci ne a karkashin wannan doka ta gwamnatin kama karya.
Duk da cewa gwamnatin mulkin sojan kasar ta sanar da ranakun sa za'a gudanar da zaben 'yan majalisar dokoki da kuma 'yan majalisar dattawa a cikin shekara mai zuwa a kasar, to amma har yanzu babu takamaimiyar ranar da za'a gudanar da zaben shugaban kasa, lamarin ke dada shakku a cikin zukatan al'ummar kasar da ke fatar samun sauyi bayan share shekaru a karkashin salon mulki na kama karya.
870016