Bangaren kasa da kasa:bayan gagaramar zanga-zanga a ranar takwas ga watan Mehr da muke ciki na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira da al'ummar kasar masar suka gudanar a dandalin tahriri a ranar juma'a a wani yunkuri na juyin juya hali komitin rikon kwarya na sojojin kasar ta Masar ya kira yi shugabannin siyasa da kungiyoyin siyasa a kasar domin yin taron gaggauwa.
Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ikna ne ya watsa rahoton cewa: bayan gagaramar zanga-zanga a ranar takwas ga watan Mehr da muke ciki na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira da al'ummar kasar masar suka gudanar a dandalin tahriri a ranar juma'a a wani yunkuri na juyin juya hali komitin rikon kwarya na sojojin kasar ta Masar ya kira yi shugabannin siyasa da kungiyoyin siyasa a kasar domin yin taron gaggauwa. Dangane da wannan lamari Alsa'id Kamil shugaban jam'iyar jabahatul Demokradiya a kasar Masar ya bayyana cewa; Sami Anan mataimakin shugaban komitin zartarwa na sojojin kasar ta Masar ya bukaci wakilan jam'iyyu da kungiyoyin siyasa na kasar a wannan zama na gaggawa su yi nazari kan duk wata bukata da ta shafi zabe da kuma ayar doka mai lamba biyar ta kundin tsarin mulkin kasar.
870477