IQNA

Kaita Hurumin Mata A Bahrain Zai Kawo Faduwar Gwamnati

Banagren kasa da kasa: Ayatullahi Isa Kasim limamin juma'a a kasar Bahrain a ranar juma'ar da ta gabata takwas ga watan Mehir na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya ya jaddada cewa; yadda gwamnatin Ali Khalifa kai cin zarafin mata da kaita hurumin mata yan juyin juya hali ba za a taba mantawa kuma wannan mataki shi ne zai yi sanadiyar da rushewar gwamnatin Ali Khalifa .



Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ikna ne ya watsa rahoton cewa: Ayatullahi Isa Kasim limamin juma'a a kasar Bahrain a ranar juma'ar da ta gabata takwas ga watan Mehir na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya ya jaddada cewa; yadda gwamnatin Ali Khalifa kai cin zarafin mata da kaita hurumin mata yan juyin juya hali ba za a taba mantawa kuma wannan mataki shi ne zai yi sanadiyar da rushewar gwamnatin Ali Khalifa . Lmamin juma'a Ayatullahi Sheikh Isa Kasim a masallacin Imam Sdaik (AS) a yankin Aldiraz na kasar Bahrain ya bayyana cewa; siyasar ta'addanci da matakan rashin imani da Ali Khalifa ke nunawa al'ummar Baharain har abada al'ummar kasar ba za su manta ba kuma ko ba komi zai kara masu karfin imani za su cimma burinsu da kifar da gwamnatin zalumci a kasar.


870407