IQNA

Goyon Bayan Palastinu Shi Ne Dalilin Matsin Lambar Kasashen Turai A Kan Iran

14:50 - October 02, 2011
Lambar Labari: 2197363
Bangaren kasa da kasa, Nabih Birri shugaban majlaisar dokokin kasar Lebanon ya bayyana cewa, babban dalilin matsin lamabar kasashen yammacin turai kan jamhuriyar musulunci ta Iran shi ne goyon bayan da take baiwa al’ummar Palastinu.
Kamfanin dilalncin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto rahoto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin din Al-alam cewa, shugaban majalisar dokokin Lebanon Nabih Birri ya fadi a wajen taron kasa da kasa na goyon bayan al’ummar palastu da boresu, wanda ake gudanarwa karo na biyar a birnin Tehran cewa, matsin lamabar kasashen yammacin turai kan jamhuriyar musulunci ta Iran shi ne goyon bayan da take baiwa al’ummar Palastinu da kuma gwagwarmayarsu.
Ya ce duk da matsin lamabar da ake kan Iran akan shirinta na makamashin nukiliya na zaman lafiya, tare da rufe idanu kan makaman nukiliya da haramtacciyar kasar Isra’ila take mallaka, amma dai babban dalilin hakan shi ne irin goyon bayan da Iran take ba wannan al’umma da ta kwashe tsawon shekaru ana zaluntar ta.
Ya ce wannan gayyata da aka yi wa masana da malamai, wata alama ce daga cikin alamomi na kiran marigayi Imam Khomeni (RA) wanda ya assa jamhuriyar musulunci ta Iran, da kuma kyakyawan jagoranci ga wannan juyi daga magajinsa.
Nabih Birri ya ci gaba da cewa, a akn wane dalili ne manyan kasashen duniya za su manta da abin da ake yi wa palastinawa na zalunci da danniya, su mayar da hankalinsu kaco kaf kan taimakon haramtacciyar kasar Isra’ila da tsaronta kawai, ya ce wannan shi ne zalunci na hakika.
870912

captcha