Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin din Al-alam cewa, a zaman taron goyon bayan gwagwarmayar palastinawa, Usama Nujaifi shugaban majalisar dokokin kasar Iraki ya yi kira da a kafa wata babbar kasuwa ta hadin gwiwa ta musulmin duniya baki daaya da nufin karfafa harkokinsu na tattalin arziki da kuma yin tasri a cikin harkokin tattalin arziki na duniya baki daya, bisa la’akari da cewa amfanin hakan zai koma ne ga al’ummar musulmi.
Ya ci gaba da cewa batun palastinu lamari mai matukar muhimamnci, ko kuma ace shi ne kan gaba a cikin dukaknin lamurran da suka shafi musulmi da larabawa da ma mutanen duniya da suke da lamiri da ‘yancin tunani.
Domin kuwa tun bayan da yahudawan sahyuniya suka mamaye yankunan palastinu a cikin shekaru kusan saba’in da suka gabata, har inda yau take, alummar wannan yanki suke ickin halin kaka ni kayi, suke cikjin wahala da rashin tabbaci.
Ya ce wajibi ne da ya rataya kan dukaknin kasashen musulmi da na larabawa da su bayar da dukaknin taimako ga al’ummar palastinu marassa kariya, da kuma nuna musu hakan a aikace ba magana ta fatar baki ba kawai da aka saba da jinta a tsawon zamani. 870902