IQNA

Halartar Kashi 10 Cikin Dari Na Mutane A Zaben Saudiyya Muhimmin Sako Ne

18:39 - October 02, 2011
Lambar Labari: 2197506
Bangaren kasa da kasa, halartar kashi goma cikin dari na mutanen da suka cancanci kada kuri’a a Saudiyya a zaben da aka gudanr a kasar a cikin makon nan babban muhimmin sako na siyasa da mahukuntan kasar ya kamata su dauki darasi daga gare shi.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin din rasid cewa, daya daga cikin fitattun malamai a kasar Saudiyya Sheikh Hassan Saffar ya bayyana cewa halartar kashi goma cikin dari na mutanen da suka cancanci kada kuri’a a Saudiyya a zaben da aka gudanr a kasar a cikin makon nan babban muhimmin sako na siyasa da mahukuntan kasar ya kamata su dauki darasi daga gare shi idan sun kasasnece masu basirar hakan.
Ya ci gaba da cewa an kwashe tsawon shekaru al’ummar kasar ba su taba sanin wani abu wai shin mulki na jama’a baki daya ba, illa dai wasu ‘yan tsiraru daga cikin jikokin Ali Saud ne rike da ragamar mulkin, inda suka mayar da dukkanin arzikin da Allah ya huwace ma kasar nasu na kansu.
A kan haka ne ya ce halartar kashi goma cikin dari na mutanen da suka cancanci kada kuri’a a Saudiyya a zaben da aka gudanr a kasar a cikin makon nan babban muhimmin sako na siyasa da mahukuntan kasar ya kamata su dauki darasi daga gare shi matukar dai suna son makomarsu ta kyau.
870782
captcha