Bangaren kasa da kasa, an gudanar da wani zaman tattaunawa tsakanin wasu masana mabiya mazhabar shi'a da kuma mabiya majami'ar katolika a banagaren nazarin mazhabar shi'a na jami'ar addinai da ke birnin Rom na kasar Italiya.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, an gudanar da wani zaman tattaunawa tsakanin wasu masana mabiya mazhabar shi'a da kuma mabiya majami'ar katolika a banagaren nazarin mazhabar shi'a na jami'ar addinai da ke birnin Rom, bisa gayyatar da shugaban wannan sashe ya yi.
Daga cikin malaman da suka halarci wannan zaman tattaunawa na kara wa juna sani hard a Muhammad taqi Ansari daga jamhuriyar Musulunci ta Iran, wanda ya gudanar da wani taron manema labarai bayan kammala zaman tattaunawar, inda ya jaddada muhimmanci ci gaba da yin hakan domin kara samun fahimtar juna.
Wannan dai ba shi ne karon farko da wannan jami'a jami'a take shirya taruka ba, domin kuwa an gudanar da wasu tarukan makamantan hakan a wasu shekarun baya, kuma sun samu halartar malamai dam asana daga kasashen musulmi da dama.
871304