IQNA

Mutanen Kasar Bahrain Ba su Fito Zaben Cike Gurbi Ba A Kasar

12:44 - October 03, 2011
Lambar Labari: 2198016
Bangaren kasa da kasa, al'ummar kasar Bahrain sun ki fitowa domin gudanar da zaben cike gurbi wanda mahukuntan kasar suka kira, domin kara nisantar da masu adawa da mulkin fir'ananci na kasar daga duk wani sha'anin siyasa.



Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto rahoto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar Al-alam cewa, al'ummar kasar Bahrain sun ki fitowa domin gudanar da zaben cike gurbi wanda mahukuntan kasar suka kira, domin kara nisantar da masu adawa da mulkin fir'ananci na kasar daga duk wani sha'anin siyasa da mulki wanda ya ginu kan nuna wariya da banbanci tsakanin mutane.

A jiya ne wata kotu a kasar Bahrain ta tabbatar da hukunci kan wasu mutane 14 da ake tsare da su saboda dalilai na siyasa, bisa hujjar cewa suna na hankoron kawo karshen mulkin mulukiya a kasar.
Dukkanin mutanen dai fitattu ne wajen gwagwarmaya ta siyasa a kasar ta Bahrain, da neman ma al'ummar kasar 'yancinsu daga mulkin mulukiya na gidan sarautar Ali-Khalifa.An yanke hukuncin daurin rai da rai a kan wasu daga cikinsu, wasu kuma daurin shekaru 15 a gidan kaso.
Kotun ta ce ta samu mutnanen da laifin tunzura mutane domin su yi zanga-zangar neman sauyi a kasar, da nufin kifar dagidan sarauta da kuma canja kundin tsarin mulki, da kuma hada baki da wasu bangarori na waje.
Wannan mataki da kotun ta dauka ya zo ne a daidai lokacin da mahukuntan kasar ta Bahrain suka kara tsananta matakan murkushe masu zanga-zangar lumana, da suke neman sauyi na demokradiyya a kasar, inda a cikin makon nan jami'an tsaron kasar Bahrain tare da na Saudiyya da suke taimaka musu, suka ci zarafin wasu mata saboda shiga cikin zanga-zangar neman sauyi, lamarin da ya jawo fushin al'ummar kasar da ma sauran musulmi a kasashen duniya daban-daban.
A cikin makonnan ne sarkin kasar Bahrain Hamad Bin Isa ya kai ziyara ta musamman zuwa kasar Saudiyya, inda ya gana da sarkin kasar da kuma wasu daga cikin masu fada a ji a Saudiyya, inda aka ba shi shawarwari dangane da yadda zai tafiyar da mutanen kasarsa da suka tsaya kai da fata suna neman mulki na demokradiyya.
Al'ummar Bahrain dai suna zargin Saudiyya da Amurka da hannu kai tsaye cikin abin da ke faruwa a kasarsu, na cin zarafin jama'a da yi musu kisan gilla, bisa la'akari da cewa Saudiyya ce ta aike da sojojinta da daruruwan tankokin yaki da motoci masu sulke zuwa Bahrain, domin murkushe zanga-zangar neman sauyi na demokradiyya da fararen hular kasar ke gudanarwa, yayin da Amurka take kare mahukuntan na Bahrain kan wannan ta'asa ta'asar da suke tafkawa. 871335
captcha