IQNA

Yahudawan Sahyuniya Sun Sake Cin Zarafin Addinin Musulunci

12:43 - October 03, 2011
Lambar Labari: 2198017
Bangaren kasa da kasa, a ci gaba da cin zarafi da keta alfarmar abubuwa masu tsarkia a cikin addinin Musulunci, yahudawan sahyuniya sun rubuta bisimillah cikakka a kan takardar goge hannu da katse majina.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin din Almanar daga kasar Lebanon cewa, domin cin zarafi da keta alfarmar abubuwa masu tsarkia a cikin addinin Musulunci, wani kamfanin yahudawan sahyuniya ya buga bisimillah cikakka a kan takardar goge hannu da katse majina domin yin amafani da ita wuraren cin abinci da makewayi.
A wani rahoton na daban kuma mai dangantaka da batun zaluncin Amurka da yahudawan sahyuniya kan al'ummar palastinu, Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya kasa cimma wata kwakkwarar matsaya kan batun neman kafa 'yantacciyar kasar Palasdinu a yayin zaman tattaunawa da ya gudanar a yammacin jiya Asabar.
A sanarwar da ya gabatar a jiya Asabar bayan kammala zaman farko na Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya kan bukatar neman kafa kasar Palasdinu da shugaban hukumar cin kwarya-kwaryar gashin kan Palasdinawa Mahmud Abbas ya gabatar a yayin jawabinsa a gaban babban zauren Majalisar Dinkin Duniya a ranar juma'ar da ta gabata; Wakilin kasar Labanon Nuwaf Salam da a halin yanzu kasarsa ce ke jagorantar matsayin shugabancin karba-karba na kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana cewa:
Dukkanin mambobin Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya goma sha biyar sun gudanar da zaman tattaunawa kan batun kafa kasar ta Palasdinu, amma zasu ci gaba da gudanar da zaman a ranar laraba.
871322


captcha