IQNA

Miliyoyin Mutane Ne Za su Taru Don Neman Rusa Yarjejeniyar Kam David

13:42 - October 04, 2011
Lambar Labari: 2198853
Bangaren kasa da kasa; An bukaci miliyoyin yan kasar masar da suka hada da kungiyoyin siyasa da masu zaman kansu da na fararen hula da na addini da kuma bangarori daban daban na al'ummar kasar ta Masar da su gudanar da gagaramin taro a dandalin tahriri na birnin Alkahira domin mukatar a yi watsi da yarjejeniyar Kamp David ta zalumci.



Kamfanin dillancin labarai na ikna ne dake kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ya watsa rahoton cewa: An bukaci miliyoyin yan kasar masar da suka hada da kungiyoyin siyasa da masu zaman kansu da na fararen hula da na addini da kuma bangarori daban daban na al'ummar kasar ta Masar da su gudanar da gagaramin taro a dandalin tahriri na birnin Alkahira domin mukatar a yi watsi da yarjejeniyar Kamp David ta zalumci.A ranar sha hudu ga watan Meher na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in ne hijira shamsiya aka bukaci kungiyoy da jam'iyun siyasa da su halarci wannan gagaramin gangami mai muhimmancin gasket domin kawo karshen wannan yarjejeniya ta zalunci da danniya da kuma wargaza ta ko al'ummomin Masar da na Palasdinu da sauran al'ummomin musulmi za su lunfasa.

872218

captcha