Kamfanin dillancin labarai na ikna ne dake kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ya watsa rahoton cewa: masu adawa da addini a baya da kuma a yanzu sun tada hankalinsu kan abubuwan da ke faruwa na sauyi da canjin da ake samu a kasashen larabawa da musulmi don haka nauyi ne ga jagororin addini na tashi tsaye domin yiwa wannan guguwar canji da farkawar musulmi jagoranci na gari.Muhsin Pakain shugaban ofishinn da ke kula da lardunan Afganistan a ma'aikatar harkokin wajen wannan kasa kuma tsowon sakataren hukumar al'adu da dangantaka ta musulmi a kungiyar hadin kan musulmi a wata tattaunawa day a yi da kamfanin dillancin labarai na Ikna ya bayyana cewa;babban abin da wannan canji a kasashen larabawa shi ne kasancewarsu musulmi kuma al'ummar wadannan kasashe musulmi ne kuma musulunci ya ratsa jinin jikinsu amma mahukumtan wadannan kasashe suna fada da musulunci da yin fito na fito da musulmi da musulunci da yin biyayya da masu adawa da musulunci a waje da ciki dalilin day a sa al'ummarsu a yau suke kalubalantarsu da kawo karshen mulkinsu da zabar abin da suke so na tsarin musulunci.
872193