IQNA

A Gobe Ne Za Gudanar Da Gagaramar Zanga-zanga Ta Manama A Kasar Bahrain

13:44 - October 04, 2011
Lambar Labari: 2198865
Bangaren kasa da kasa:Hadin guiwar matasan juyi na sha hudu ga watan Fevreru a Bahrain e suka fitar da wata sanarwa da a ciki suke kira ga al'ummar kasar Baharian da su fito a gobe sha biyu ga watan Mehr na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in domin gudanar da wata gagaramar zanga-zanga a kan titunan birnin Manama a zanga-znagra da aka bata sunan Tufanar Manama.


Kamfanin dillancin labarai na ikna ne dake kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ya watsa rahoton cewa: Hadin guiwar matasan juyi na sha hudu ga watan Fevreru a Bahrain e suka fitar da wata sanarwa da a ciki suke kira ga al'ummar kasar Baharian da su fito a gobe sha biyu ga watan Mehr na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in domin gudanar da wata gagaramar zanga-zanga a kan titunan birnin Manama a zanga-znagra da aka bata sunan Tufanar Manama.Al'ummar kasar za su fito domin nuna damuwa da kuma bayyana ra'ayinsu da bacin ransu kan zalumcin gwamnatin kasar Baharain da irin kisan gilla da gallazawar da ta ke nunwa al'ummar kasar faraen hula masu gudanar da zanga-zangar nuna rashin jin dadinsu da gwamnatin kasar.

872176

captcha