IQNA

Faransa Za Ta Daukin Bakuncin Taro Kan Tsananin Ra'ayin Addini

Bangaren kasa da kasa:Za a gudanar da taro kan masu tsananin ra'ayin addinin musulunci ina suka dosa da hadin guiwar kungiyoyin koyar da ilimi da mu'assisho masu nazarin ilimomin addinin musulunci a Faransa suka shirya.



Kamfanin dillancin labarai na ikna ne dake kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ya watsa rahoton cewa: Za a gudanar da taro kan masu tsananin ra'ayin addinin musulunci ina suka dosa da hadin guiwar kungiyoyin koyar da ilimi da mu'assisho masu nazarin ilimomin addinin musulunci a Faransa suka shirya.Wannan shi ne irinsa na farko da za a gudanar da irin wannan taro a kasar ta Faransa tare da halartar shugabanni da wakilan kungiyoyin da lamarin ya shafa a cikin kasar ta Faransa da kuma wasu daga kasashen Larabawa da na musulmi a wasu nahiyoyin na duniya>Masana da manazarta za su tattauna da yin nazarin hanyoyi da dalilin da ke sawa tsananin addinin musulunci a duniya.

872173