Bangaren kasa da kasa: babban mai bada fatawa a kasar Suriya a lokacin jana'izar dansa day an ta'adda suka yi masa kisan gilla a wani harin ta'addanci ya jaddada cewa: wadanda ke kai hare-haren ta'addanci a kasar Suriya ba suna kai hari ne kan wani mutum a karan kansa ba a'a burinsu al'umma da kasar Suriya baki daya domin kaskantar da ita a gaban haramtacciyar kasar Isra'ila.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna ne da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; babban mai bada fatawa a kasar Suriya a lokacin jana'izar dansa day an ta'adda suka yi masa kisan gilla a wani harin ta'addanci ya jaddada cewa: wadanda ke kai hare-haren ta'addanci a kasar Suriya ba suna kai hari ne kan wani mutum a karan kansa ba a'a burinsu al'umma da kasar Suriya baki daya domin kaskantar da ita a gaban haramtacciyar kasar Isra'ila da Amerika.A ranar sha daya ga watan Meher ne na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya aka yi masa jana'izar tare da sakon shugaban kasar ta Suriya ,jana'izar da dubban yan kasar ta Suriya suka halarta domin nuna juyayinsu kan wannan danyan aiki na dabbanci da rashin hankali da kuma yi wa makiyan musulmi da musulunci hidima.
873024