IQNA

Shugaban Hukumar Al'adu Na Musulunci Ya Ziyarci Ikna

14:31 - October 05, 2011
Lambar Labari: 2199558
Bangaren kasa da kasa: Mahummad Bakir Khurramshahar shugaban hukumar da ke kula da harkokin al'adu da dangantaka ta musulunci tare da wata tawaga da ke mara masa baya ya ziyarci kamfanin dillancin labarai na Ikna mai kula da harkokin kur'ani inda ya ganewa idonsa yadda suke gudanar da ayyukansu a fannoni daban daban.



Kamfanin dillancin labarai na Ikna ne da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa;Mahummad Bakir Khurramshahar shugaban hukumar da ke kula da harkokin al'adu da dangantaka ta musulunci tare da wata tawaga da ke mara masa baya ya ziyarci kamfanin dillancin labarai na Ikna mai kula da harkokin kur'ani inda ya ganewa idonsa yadda suke gudanar da ayyukansu a fannoni daban daban. A lokacin wannan ziyara ya samu rakiyar Hujjatul Islam da musulmi Said Mahdi Takwa shugaban riko na na kamfanin dillancin labarai na Ikna da kuma wasu shugabannin bangarori daban daban na hukuma inda ya ganewa idonsa irin kokarin da wannan kamfani yake yi musamman bangaren labarai na kasashe daban daban na kasa da kasa,bangaren adabi ,da kuma na kananan yara da matasa.,siyasa da zamantakewa da sauran fannoni na kamfanin.

873125

captcha