Kamfanin dillancin labarai na Ikna ne da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; a daidai lokacin da al'ummar birnin Manama fadar mulkin kasar Bahrain ke gaf da fara wata gagaramar zanga-zanga da aka bawa taken Dufanar Manama jami'an tsaron gwamnatin Ali Khalifa masu yawan gasket sun mamaye da jibge su a kan titunan da masu zanga-zanga za su bi. A jiya ne kungiyoyin siyasa da kuma kungiyoyin fararen hula a kasar ta Bahrain suka bukaci al'ummar kasa da su fito kan tituna domin fara wata gagaramar zanga-zanga mafi girma domin nuna bacin ransu da kuma neman kawo sauyi da canji a harkokin jagoranci da zamantakewa da siyasa kasar . Amma a duk lokacin da suka fito kan titunan suna fuskantar takurawa da nuna karfi fiye da kima da kisan gilla na rashin tausayi da dabbanci daga jami'an tsaro na kasar ta Bahrain a daidai lokacin da duniya day a hada da kungiyoyi na kasa da aksa da hukumomi suka yi gum da bakinsu bas u cewa uffin kan wannan danyan aiki.
873017