IQNA

Ma'aifar Kaddafi Ta Fada Hannun Yan Tawaye A Libiya

14:30 - October 05, 2011
Lambar Labari: 2199566
Bangaren kasa da kasa: daga karshe dai ma'aifar Mu'ammar Kaddafi tsohon shugaban kasar Libiya ta fada hannun masu bore da kokarin kawo canjin mulki a kasar ta Libiya .

Kamfanin dillancin labarai na Ikna ne da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; daga karshe dai ma'aifar Mu'ammar Kaddafi tsohon shugaban kasar Libiya ta fada hannun masu bore da kokarin kawo canjin mulki a kasar ta Libiya.A ranar juma'ar da ta gabata ne Mustapha Abdul Jalil shugaban komitin zartarwa na masu juyin juya hali a kasar ta Libiya ya bawa mazauna garin Sirt sa'o'I arba'in da takwas da su fice daga garin kuma a dabra da haka a wani taron manema labarai day a yi a Bangazi ya bayyana cewa; bayan kwanaki biyu na tattaunawa komitin day a ke jagoranta ya amince da kawo gyara a jerin zartarwa tare da kawo canji kuma Jibril ya canja ra'ayinsa kan yin marabus daga matsayinsa na shugaban ofishin zartarwa har zuwa lokacin intar da libiya baki daya.

872959

captcha