Bangaren kasa da kasa:A daren jiya ne sha daya ga watan Meher na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya bayan wani rikici mai tsanani day an shi'a mazauna garin Al'awamiya a lardin Katif yan sanda a kasar Saudiya suka yi awan gaba da wasu daga cikin yaya kungiyar kare hakkin dan adam.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna ne da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; A daren jiya ne sha daya ga watan Meher na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya bayan wani rikici mai tsanani day an shi'a mazauna garin Al'awamiya a lardin Katif yan sanda a kasar Saudiya suka yi awan gaba da wasu daga cikin yaya kungiyar kare hakkin dan adam.Yan Sandan sun yi awangaba da Haji Hasan Al Zadyid da haj Said AbdulAl karkashin zargin ya yansu sun shiga a cikin zanga-zangar da al'ummar kasar suka gudanar yayin da shi kuwa Fadil Almanasif day a tafi ofishin yan sanda domin bin diddigin lamarin aka tsare shi,shi ma.
872928