IQNA

Yahudawan Sahyuniya Sun Rufe Masallacin Annabi Ibrahim (AS)

16:13 - October 06, 2011
Lambar Labari: 2199989
Bangaren kasa da kasa, yahudawan sahyuniya sun rufe masallacin annabi Ibrahim (AS) da ke garin Alkhalil tare da hana dubban palastinawa yin salloli a cikinsa kamar dai yadda rahotanni daga yankin suka tabbatar.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto wani rahoto daga shafin sadrawa na yanar gizo ism-france cewa, jami’in da ke kula da harkokin addini na yankin khalil Zaid Aljabbari ya sheda cewa, a ci gab ada tsokanar musulmi palastinawa yahudawan sahyuniya sun rufe masallacin annabi Ibrahim (AS) da ke garin Alkhalil tare da hana dubban palastinawa yin salloli a cikinsa ranar jiya baki daya.
Ya ci gab ada cewa yahudawan wadanda dukkaninsu ‘yan share wuri zauna ne da suke zaune a wasu matsugunnai da suke kusa da yankin, sun shigo garin khalil dauke da makamai, inda suka rufe dukkanin kofofin masallacin, wadanda musulmi suke shiga domin isa zuwa ga babban ginin, inda suke yin salla.
Yahudawan sahyuniya sun rufe masallacin annabi Ibrahim (AS) da ke garin Alkhalil tare da hana dubban palastinawa yin salloli a cikinsa ne domin tsokanar musulmi, tare da nuna girman kai da halin isa, domin kuwa sun tabbatar da cewa babu abin zai same su domin kuwa kasashen yammacin turai za su goyi bayansu kan hakan.
873915

captcha